ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-Aqsa ta nakalto Jibril Arrajoob sakataren gudanarwa na jam’iyyar Fat ta Falasdinawa yana fadar haka a jiya Alhamis. Ya kuma kara da cewa, kungiyoyin Falasdinawa sun gudanar da taron nasu a kasar Turkiya sannan sun cimma matsayi a kan ci gaba da gwagwarmaya tare da tawakkuli da All.. da kuma mutanensu har zuwa lokacin da za’a kafa kasar Falasdinu mai cikekken ‘yanci wacce kuma birnin Qudus zai kasance babban birnin ta.
Jibril ya kammala da cewa nan da ranar daya ga watan Octoba mai kamawa shuwagabannin Falasdinawa, karkashin jagorancin Mahmood Abbas , zasu fitar da cikekken sabon tsari na ayyukan kungiyoyin Falasdninawa a gwagwarmayan da suke yi da Haramtacciyar kasar Isra’ila.
342/